Sama da kwana 30 gwamnati ta san za a yi zanga-zangar nan. Me gwamnatin tayi? Sai gayyatar malamai da shugabannin gargajiya su zo su gayawa mutane cewa zanga-zanga babu kyau ko kuma kada a yi zanga-zanga. Mutane suna kwana da yunwa, basa zuwa makaranta, ana sace mutane ana kashe su ana yi wa mata fyaɗe saboda gazawar gwamnati. An ce za a yi zanga-zanga, amma gwamnati ta tsaya tana nemo hayar talakawa tana ce musu su fito su ce suna goyon bayan gwamnati. Babu jami'an tsaro da yawa, mutane sun yi musu yawa, kuma waɗannan matasan su ne ya kamata a ɗauka aikin tsaron. Gwamanti za ta ɗauki aikin jami'an tsaro amma ƴan siyasa su ne suke zuwa su ce a basu offer aikin su rabawa waɗanda suka ga dama ko su siyar. Gwamnati sai ƙarya take yi wa mutane za ta siyar da shinkafa a kuɗi kaza da sauransu. Shugaban ƙasa tun kafin ya shiga office, a wajen da aka rantsar da shi ya saka mutane a masifa, ya ce ya janye tallafin man fetur, wasu matsalolin tun daga wannan ranar suka fara. Ku bayar da dama mutane su samu abincin su ci, ku samar musu da tsaro, ku basu damar zuwa makaranta cikin sauƙi. Ku dawo da tallafi ku buɗe hanyoyin shigo da kayan abinci. Ba wanda za ku gani a kan titi da sunan zanga-zanga. Shekara nawa kuna abin da kuka ga dama? Babu wanda ya yi muku bore, sai yanzu da kuka saka mutane cikin yunwa da talauci da halin rashin tsaro.
@sainafada1gyyakub
Ай бұрын
Hmmmm Allah Yasa Mudace
@AbbaDanmusa-nz3ey
Ай бұрын
Baban ka ne kai kadai
@arufi-autah
Ай бұрын
A yanka mana shi ta gaba ta baya sai kace wasu matsorata😒
@user-rn4mf1zw7y
Ай бұрын
😂😂😂😂😂
@umarmusahaddabi8888
Ай бұрын
in Sha Allah sakonka zai Kai garesu Amma sai Wanda ya fahimta da kew zai gane batunka Allah ya Kara fasaha don isar Mai esa fiyeyen halitta Baki dai
@FatimaJibrin-ke2xz
Ай бұрын
Allah yakawo mana wannan ranan
@FatimaJibrin-ke2xz
Ай бұрын
Dan shekara 100 nata bamu wahala Allah yakawo lokacin tafiyarka lahira tinibu
Пікірлер: 27